Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Bada Sanarwar Karin Takukunmi Ga Kasar Rasha


Amurka ta ba da sanarwar karin takunkumai ga kasar Rasha, a dalilin ci gaba da goyon bayan ‘yan tawayen kasar Ukraine da kuma hade yankin Crimea da ta yi.

Babban bankin Amurka ya fada a wata sanarwa da ya fitar jiya Alhamis, ta saka wasu karin mutane har 37 da kamfanoni dake a yankin Crimea da Ukraine cikin wadanda za a kakabawa takunkumi.

Kamar yadda babban bankin yace, wannan ya biyo bayan ci gaban takunkumin da kungiyar Tarayyar Turai ta yi, kuma hada wadannan matakai na nuna cewa kasashen duniya basa goyon bayan abin da Rasha ta ke yi a Ukraine.

Kamfanonin Rasha ciki har na kamfanin gine gine na PJSC Mostotrest da SGM an saka su cikin wadanda za a kakabawa takunkumin, a saboda taimakon da suke bayarwa na gina Gada daga Rasha zuwa yankin Crimea.

XS
SM
MD
LG