Rundunar Sojin Najeriya Ta Nuna Takaicinta Kan Hare-haren Borno

Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta yi bakin cikin gaske bisa kisan
gilla da yan ta'addan Boko Haram suka yi wa mata da kananan yara a kauyen Faduma Kolloram da ke yankin Gubio a jihar Borno.

Hedkwatar sojojin Najeriyar ta ce ta aike da karin dakaru na musamman a
wannan yanki don kamo ko kashe duk 'yan ta'addan da suka tafka wannan
aika-aika.

Sanarwar da Kakakin sojojin Najeriyar Kanar Sagir Musa ya aikewa
Muryar Amurka, ta ce tuni an umarci babban kwamandan rundunar
"Operation Lafiya Dole" mai yaki da Boko Hara a shiyyar na arewa maso gabas da ya tabbatar sojoji sun mamaye wannan yanki don tabbatarwa mutanen wurin irin damuwar dakarun ga tsaron lafiyarsu.

Bugu da kari, hedkwatar sojojin Najeriyar ta kuma nuna damuwa bisa kashe
kashen da yan bindiga dadi sukai a jihohin Katsina, Zamfara da Sokoto
inda tace yan bindigar na hushe haushi ne akan irin barin wuta da take
masu cikin dazuka.

Hedkwatar sojojin tace yayin da take jajentawa mitanen jihohin da
kashe kashen ya shafa, tace tana nan tana aiki tukuru don kawo karshen
tu'annatin yan bindigar da kuma samar da kwanciyar hankali.

Yayin da sojojin ke cewa za a binciki musabbabi kashe-
kashen na baya bayan nan, sojin na kasa sun ce suna nan suna kara tsara
aiki tare da rundunar sojojin sama don rugurguza dukkannin sansanonin
'yan ina-da-kisan,

Akan haka ta ce tuni ta ma tura karin dakaru da kayan aiki don yi wa
tufkar hanci kamar yadda shugaba Muhammadu Buhari ya ba da umarni a
kwanannan.

Hedkawatar sojojin ta tabbatarwa 'yan Najeriya cewa irin
wannan kashe-kashe lalle ba zai kara faruwa ba, don tana nan tana shirin
daukar mataki.

Saurari karin bayani a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Rundunar Sojin Najeriya Ta Nuna Takaicinta Kan Hare-haren Borno