Rundunar Sojin Najeriya ta Bayyana Nasarorin da Take Samu kan Boko Haram

Sojojin Najeriya

Kanar Kuka Sheka ya bada haske akan irin nasarorin da rundunar sojin Najeriya take samu kan 'yan ta'adan Boko Haram

Sojojin Najeriya suna dadakutsawa cikin dajin Sambisa inda 'yan ta'adan Boko Haram suka kafa sansanoninsu.

Ana kokarin tarwatsa duk sansanoninsu a kawar dasu gaba daya.

Kawo yanzu sojojin sun rusa wasu sansanonin 'yan ta'adan har guda takwas musamman a bangaren Bama. Banda makamai da mashina da sojojin suka kama har ma sun kama wani babban kwamanda na 'yan ta'adan.

Rundunar ta kuma kubutar da wasu mutane 178 da 'yan Boko Haram suka sace. Cikin mutanen 101 yara ne. Akwai mata 67. Maza kuma 10.

Rundunar sojin ta kira 'yan Najeriya su cigaba da ba jamai'an tsaro musamman sojoji goyon baya. Yakin da ake yi da 'yan ta'ada abu ne na kasa baki daya.Jama'a su taimaka ta fuskar bada bayanai da kuma kula da muhalli da makamantansu saboda cimma nasara gameda yakin.