Rundunar Tsaro Ta Kaddamar Da Yaki Da Miyagun Ayyuka A Plato

Hoton mika rahoton kwamitin tsugunar da wadanda rikici ya shafa a Plato

Rundunar gake wanzar da zaman lafiya a jahar Pilato, ta kudiri aniyar yaki da masu aikata laifuka da suka hada da kungiyoyin asiri, sara-suka, shan miyagun kwayoyi da wassu laifukan da bata ari ke aikatawa

Kwamandar rundunar STF, Manjo Janar, Augustine Agundu yayin paredin wassu ishirin da uku da aka kama ake zargi da fashi da makami, ayyukan asiri, da ta’addanci, yace jami’ansu sun tashi tsaye wajen bankado duk masu laifi a fadin jahar Pilato.

Shugaban hukumar inganta zaman lafiya a jahar Pilato, Joseph Lengman ya bayyana takaicinsa kan muggan laifuka inda ya bukaci hadin kan kowa don magance su.

a cikin hirarsa da Sashen Hausa, Evangelist Jerry Datim dake taimaka wa matasa, su gyara halinsu, ya ce dole iyaye su bada goyon baya wajen bankado masu laifi.

Shi kuwa a nasa bayanin Malam Sani Suleiman dake aikin inganta zamanta kewar al’umma yace hukuma ta jajirce wajen hukunta masu laifi.

Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji.

Your browser doesn’t support HTML5

An dauki matakan tsaro a Plato-3:00"