Shin Ya Kamata Buhari Ya Yi wa Gwamnatinsa Garambawul?

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a tsakiya sanye da fararen kaya, bayan daya dawo daga jinyarsa ta farko da ya je London a watan Maris din 2017

A Najeriya ana ci gaba da kiraye-kiraye kan cewa lokaci ya yi da shugaba Muhammadu Buhari zai yi wa gwamnatinsa kwaskwarima.

Batun kiraye-kiraye da ake yi na neman shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi sauye-sauye a gwamnatinsa na janyo ka-ce-na-ce tun bayan da shugaban ya dawo daga jinya a London inda ya kwashe sama da watanni uku.

Wannan korafi da mutane ke gabatarwa na zuwa ne yayin da gwamnatin ta APC ta kwashe sama da shekaru biyu akan karagar mulki.

A lokacin yakin neman zabe, jam’iyar APC, ta yi alkawarin kawo sauyi daga irin mulkin da ‘yan kasar suka gani a zamanin mulkin babbar jam’iyar adawa ta PDP.

To amma kiraye-kirayen da ake yi na cewa shugaban ya sauya wasu ministocinsa na ci gaba da karuwa.

Yanzu haka kungiyar kwadago ta NLC ta kasa ta shiga jerin bangaren da ke kiran a sauya wasu ministoci domin a cewarta wasunsu babu abinda suka tabuka.

Shugaban kungiyar ta NLC, Comrade Ayuba Wabba ne ya bayyana hakan yayin wata hira da ya yi da wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka Hassan Maina Kaina.

Masana kimiyyar siyasa irinsu Dr. Abubakar Umaru Kari, su ma sun bi sahun wannan kiraye-kirayen, inda ya ce tunda an kwashe shekaru biyu, ya kamata a kawo wasu su ba da ta su gudunmuwar.

Saurari rahoton Hassan Maina Kaina domin jin cikakken abinda dukkanninsu suka fada:

Your browser doesn’t support HTML5

Shin Ya Kamata Buhari Ya Yi wa Gwamnatinsa Garambawul? - 2'29"