Shugaba Buhari Ya karbi Wakili Na Musamman Daga Afirka Ta Kudu

Shugaban kasan Najeriya Muhammadu Buhari da Mista Jett Radebe

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya karbi bakuncin wakili na musamanman Mista Jett Radebe da shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya aika a fadarsa dake Abuja.

Shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa ya aika da wakili na musamman zuwa Abuja, domin ganawa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, da kuma tattaunawa game da tashe tashen hankullan da ya afku a hare haren da masu kyamar baki a Afirka ta Kudu suka kaiwa ‘yan Najeriya.

Wannan ziyara wani mataki ne da Shugaba Ramaphosa yake ‘dauka domin warware matsalar demokaradiyyar dake neman dabaibaye kasar sa.

Kasashen Afirka bakwai ne wakilan musamman za su ziyarta, bayan sun fara mayar da martani akan abin da ya faru da ‘ya’yan kasar su a can Afirka ta Kudun a watan da ya gabata.

A saurari cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Umar Faruk Musa.