Shugaba Jonathan Yace Zai Habaka Noma a Jihar Kano

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, 11 ga Disamba 2014.

Shugaban kasan yace Kano jiha ce data yi fice wajen ilmi da noma da kuma kasuwanci.

Shugaban Najerya Goodluck Ebele Jonathan, yayi alkawarin zai habaka aikin noma daya daga cikin sana'o'i da aka san jihar kano, ba domin wadata a abinci a cikin kasa ba, amma domin sayarwa a kasashen waje.

Shugaban na Najeriya yayi wannan alkawarin ne lokacin da tawagar yakin neman zabensa ta isa jihar kano inda yayi alkawarin zai habaka wannan sashe, ga kuma ilmi da kasuwnci fannoni da aka san jihar dasu.

Da yake jawabi, mataimakin shugaban kasa Alhaji Muhammadu Namadi Sambo, ya karyata zargin da ake yiwa gwamnati cewa da hanunta a cikin tashe tashen hankulan da ake yi. Yace babu yadda za'a yi gwamnati wacce ta san zafin kanta da zata juya tana kuma kashe 'ya'yanta.

Shugaba Goodluck Jonathan ya kuma ziyarci fadan maimbartaba sarkin kano Alhaji Sanusi na biyu. A jawabinsa sarki Sanusi yace, dalilin demokuradiyya shine baiwa 'yan kasa 'yancin su zabi mutane da zasu shugabance su.

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaba Jonathan Zai Habaka Noma a Kano