Accessibility links

Guguwar Sauyi Tana Kadawa a Jihar Taraba


Sanata A'isha Jummai Alhassan 'yar takarar gwamnan Taraba a inuwar APC.

Dimbin magoya bayan jam'iyyar APC suka taru a wani gangamin kaddamar da mataimakin 'yar takarar gwamnan jihar.

Elder John Maigari Ekin daga karamar hukumar Takum mahaifar dan karar gwamna a karkashin jam'iyyar PDP Mr. Darius Ishaku shi ne mataimakin 'yar takarar.

A gangamin, kungiyoyin mata sun nuna farin cikinsu domin a wannan zabe mai zuwa mace zata kara da maza wurin neman kujerar gwamnan jihar. Sanata Aisha Jummai Alhassan ita ce 'yar takarar kujerar gwamnan daga APC.

Matan sun gargadi duk waadanda suka kasance wurin gangamin su kai sako. Su shirya su fito ranar zabe su zabi Sanata Aisha. Kada suyi APC da baka kawai.

Dr. Abdulmunmuni Baki wanda yayi shugabancin jam'iyyar PDP a jihar na kusan shekaru goma yace bana kam guguwar sauyi ce ke kadawa ba wai kawai a jihar Taraba ba amma a duk fadin Najeriya. Ya kira magoya bayan APC su tashi tsaye su tabbatar sun hana magudin zabe da aringizon kuri'u. Yace su a APC basu da shirin yin magudi. Talakawa sun karbesu kuma da sonsu suke tsayawa takara.

Ita 'yar takarar Sanata Aisha ta mayarda martani ne akan korafe-korafe da wasu keyi a kanta. Tace taji wasu suna cewa bata da miji. Tace ita matar aure ce. Mijinta mutumin jihar Neja ne kuma sunansa Injiniya Sani Alhassan. Yayi ritaya daga aikin gwamnati yana zaune a Suleja. Tace mijinta ba mijin hajiya ba ne da dinga binta zoi-zoi koina zata.

Dan takarar gwamnan jihar na PDP yace guguwar sauyin bata damesu ba. Alhaji Abubakar Bawa daraktan kemfen na dan takaran PDP yace idan Allah ya yadda jam'iyyarsu zata samu nasara.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.


XS
SM
MD
LG