Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar 'Yansandan Jihar Rivers Tayi Taro da Shugabannin Siyasar Jihar


Gwamnan jihar Rivers Rotimi Amechi.
Gwamnan jihar Rivers Rotimi Amechi.

Manufar taron shi ne domin cimma matsaya daya kan yadda za'a gudanar da kemfen da kuma zabuka cikin kwanciyar hankali da lumana.

Yanzu ana iya cewa yakin neman zabe a jihar ya zama tamkar yakin Badar a jhar.

Lamarin ma ya fi tsamarin a tsakanin jam'iyyun PDP da APC domin lamarin tuni ya koma na kai hare-hare kan juna inda duka bangarorin kan yi anfani da nakiya ko bom ko bindiga. Hare-haren suna kaiga salwantar rayuka da dukiyoyi.

Taron da rundunar 'yansandan ta kira ya tattaro mutane 22 daga yam'iyyu da magoya bayansu. Rundunar tana son cimma yarjejeniyar zaman lafiya a lokacin zabukan da kuma bayan an bada sakamako.

Taron ya gudana cikin yanayin tada jijiyoyin wuya da yamutsa hankali musamman taskanin APC da PDP inda kowace na zargin an kai mata hari. Wadannan jam'iyyu su suka mamaye tattaunawar.

Philip Abuwa shugaban jam'iyyar PDP a jihar ya zargi APC da haddasa rikici. Ya kara da cewa su ba zasu kyalesu ba. To amma APC ta dade tana zargin rundunar 'yansandan da nuna rashin adalci tsakaninta da PDP. Tace ita mai bin doka ce.

Shugaban APC Dr Akanya ya musanta zargin da PDP tayi da kuma zargin cewa jam'iyyarsu bata mutunta rundunar 'yansandan. Yace shi bai taba cewa bai amince da 'yansandan Najeriya ba. Amma yace shi ya san yace a bar 'yansamda suyi aikinsu kamar yadda doka ta tanada.

Dan Bature kwamishanan rundunar yace suna son su gane zabe ba maganar yaki ba ne. Siyasa ce kuma zasu ba kowa tsaro su tabbara sun yi abun da yakamata suyi cikin lumana. Su na son shugabannin 'yan siyasar su wayar da kawunan magoya bayansu akan yadda ake gudanar da harkokin siyasa. Siyasa ba fada ba ce kuma ba yaki ba ne.

SAUTI: Rundunar 'Yansandan Jihar Rivers Tayi Taron da Shugabannin Siyasar Jihar -3' 35" http://bit.ly/1ukeYOJ

HOTO: Rotimi Amechi Gwamnan Jihar River

#Hausa #Nigeria

Ga rahoton Lamido Abubakar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:35 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG