Shugaban Kasar Nijar Da Jakadan Amurka Sun Jagoranci Bikin Raya Gonakai

Shugaban kasar Nijar Issouhou Mahamadou ya jagoranci bikin fara ayyukan raya DAM ko gandari na Birni N'Konni tare da jakadan kasar Amurka a Nijar, da shugaban asusun MCC na Amurka, da ta baiwa Nijar kyautar tsabar kudi miliyan 250 na sefa da za'a kashe a tsawon shekaru 5 domin raya sha'anin noma.

Daga cikin su, sefa sama da biliyan 40 za a kashewa DAM ko gandarin Birni N'Konni domin raya shi, tare da bunkasa noma wa maza da mata tare, da cudanyawa da nakasassu, haka ma hanawa matasa tafiya ci rani kasashen waje ko neman zuwa Turai, suna rasa rayukansu a sahara ko teku.

A jawabin shugaban MCA Nijar da na jakadan kasar Amurka, da na Sim Kean Pross shugaban Millenium Challenge of corporation na Amurka, da ta tallafawa Nijar domin raya gonakai sama da dubu 2 da 500 da zai shafi manoma sama da mutun dubu 10, sun yi farin cikin ganin wannan rana, tare da yiwa al'ummar Birni N'Konni barka da samun wannan tallafin na kasar Amurka.

Ministan gidan gona Albade Abuba yayi jawabin kaddamar da aikin a wurin bukin da ya samu halartar sarakunan gargajiya, magajinan gari, ministoci, 'yan majalisun dokoki na kasa, da shugaban gundumar Birni N'Konni, da mataimaki na farko na majalisar dokoki ta kasa, da babban wakilin shugaban kasa, da sauran shugabanin hukumomi na Nijar, da Gwamnan jihar Tahoua.

A rahoto a sauti daga wakilin Muryar Amurka Harouna Mamane Bako.

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaban Kasar Nijar Da Jakadan Amurka Sun Jagoranci Wani Gagarumin Buki