Siyasar Kano: Kwankwaso Ya Kai Wa Shekarau Ziyara

Tsohon gwamnan jihar Kano, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso

A 'yan kwanakin nan, gabanin karatowar zabukan fidda gwani salon siyasar jihar Kano a Najeriya ya sauya salo, tsakanin bangaren gwamna Ganduje da bangaren Malam Ibrahim Shekarau.

Kano, Nigeria - A dai makon da ya wuce ne gwamna Ganduje ya kai wa Malam Shekarau ziyara ta ba-zata, kwatsam sai ga shi tsohon gwamna kuma jagoran jam'iyyar NNPP shi ma ya kai wa malam Ibrahim Shekarau ziyara a wani yunkurin zawarcinsa ga jam'iyyarsa.

A yayin da rikici tsakanin manyan ‘yan siyasar jihar ta Kano ke sake daukar sabon salo, a wannan makon jihar ta dau zafi a lokacin da gwamna Abdullahi Umar Ganduje da tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso kowannensu ke kokarin janyo sanata Ibrahim Shekarau a siyasarsa.

A yanzu haka dai tauraron malam Ibrahim Shekarau ke haskawa, inda ya ke kokarin maida hankalinsa a jam'iyya daya, wato ko dai ya zauna a jam'iyyarsa ta APC ko ya sauya sheka.

A jiya Lahadi ne dai Rabiu Musa kwankwaso ya kai wa malam Ibrahim Shekarau ziyara domin zawarcinsa. Tun da farko dai yaran Kwankwaso ne suka fara kai wa malam Ibrahim Shekarau ziyara.

Da ya ke magana a lokacin ziyarar, Kwankwaso ya ce ko wa ya sa halin da jihar Kano ke ciki a yanzu, shi ya sa suke kokarin maida alkiblarta yadda ya kamata.

Shi ma malam Shekarau ya bayyana cewa akwai bukatar a hada hannu don tallafawa na baya saboda ci gaban jihar Kano.

Tuni dai ake da masaniyar cewar bangaren malam Ibrahim Shekarau da gwamna Ganduje ke 'yar tsama, a makon da aka yi bankwana da shi gwamna Ganduje ya kai ziyarar ba-zata ga Sanata Ibrahim shekarau ko da yake ziyarar bata cimma nasaraba.

Saurari rahoton Baraka Bashiri:

Your browser doesn’t support HTML5

Ziyarar Kwankwaso ga Shekarau