Sojoji Sun Hambarar Da Gwamnatin Mohammed Mursi

Egyptian Defense Minister Abdelfatah al-Sissi delivering a statement on July 3, 2013 as the army unveils a roadmap for Egypt's political future. (Egyptian TV photo)

Babban Hafsin Hafsoshin kasar Masar ya dakatar da kundun tsarin Mulkin Kasar, kuma ya bayyana cewa shugaban kotun kasar, shine aka zaba a matsayin shugaban kasa na rikon kwarya.
A wani jawabi da yayi wanda aka watsa a gidan talabijin na kasa a yammacin yau Laraba, shugaban dakarun kasar Abdul Fatah Khalil Al-Sisi yace sojojin kasar sun amsa kiran mutan Masar ne, bayan gagamin adawa da mutane suka yi tayi suna kira Morsi ya sauka daga kan karagar mulki.

Sojojin sun shata wa Mr. Morsi sa’a’o 48 domin warware takadammar siyasa ko ya fuskanci juyin mulki. Manyan Hafsoshin soji sunce zasu wallafa wani fasali irin nasu idan gwamnatin Muslim Brotherhood basu cimma dai-daituwa ba da abokan adawarsu kafin karfe biyar na yamma, agogon Misra.