Accessibility links

Hukumar Leken Asirin Amurka tana samamen kasashen Yammacin Turai da ofisoshinsu a Washington DC da New York

Hukumar leken asiri ta Amurka tana samamen kasashen Yammacin Turai da ofisoshinsu a Washington DC da New York da ma Brussels.

Ranar Lahadi wata mujallar kasar Jamus ta fitar da wani rahoto da tace dan Amurkan nan da ake zargi da fallasa aikin hukumar leken asirin Amurka ne ya bata. A cikin takardun da yaba mujallar ya ce Amurka tana kai samame kan hanyar sadarwar kasashen Yammacin Turai da ofisoshinsu dake New York da kuma ofisoshin 'yan majalisar Turai a birnin Brussels. Edward Snowden shi ne wanda Amurka ke farauta yanzu domin wannan fallasa na yadda Amurka ke gudanar da aikin leken asiri ta sauraren hanyoyin sadarwa da na aika sakon hanyar yanar gizo.

Shugaban majalisar Turai ya ce wannan abun mamaki ne kuma abu ne da ya girgizashi. Kasashen Faransa da Jamus sun bukaci cikkaken bayani daga hukumomin Amurka kan wannan zargi. Shugaban majalisar Turai din ya yi nuni da irin illar da lamarin zai kawo game da dangartakarsu da Amurka. Ya ce nan da 'yan kwanaki masu zuwa Tarrayar Turai zata shiga tattaunawa da Amurka game da sha'anin cinikayya amma ga 'yan majalisa kamar sa abun takaici ne. Ya ce ga mu masu neman komawa shawarwari da Amurka kan cinikayya abun zai yi mana wauya a halin da ake ciki yanzu. Ya kara da cewa babban abun takaici ne a ce kasar da suka dauka abokiyarsu na yi masu zagon kasa ta hanyar leken asirinsu.

Dan majalisar adawa a majalisar dokokin kasar Jamus ya ce lalle tilas Amurka ta bayyana matsayinta a wannan lamarin abun kunya. Shi kuma dan majalisa daga bangaren gwamnatin Jamus cewa ya yi akwai bukatar binciken lamarin cikin gaggawa domin mumunan sabanin da ka iya faruwa.

Sani Dauda nada rahoto.

XS
SM
MD
LG