Sojojin Najeriya Sun Ceto Wasu Mutane Daga Hannun 'Yan Boko Haram

Wadanda Aka Ceto Daga 'Yan Boko Haram

A wani farmakin da ta kai, rundunar sojojin Najeriya ta ceto wasu mutane ciki har da mata da kananan yara kimanin su 31 daga mayakan Boko Haram.

Jami'in sadarwa na aikace-aikacen rundunar, Kanar Aminu Ilyasu, ya bayyana cewa wannan ya biyo bayan wani mummunan farmaki ne da dakarun suka kai a wani babban sansanin mayakan Boko Haram.

Dakarun sun yi amfani da jirgin leken asiri mara matuki ne, ta haka suka gano sansanin, inda nan take suka diram masu, suka kuma yi rugu rugu da su.

A sakamakon wannnan farmaki, sun kwato tarin makamai iri daban daban, da dimbin harsasai masu yawan gaske, sannan sun kuma ceto wadannan mutane.

Kazalika, dakarun Najeriya sun fatattaki karin mayakan na Boko Haram a wurare irinsu Criss Kauwa, Malamfatori, da dai sauran wurare a yankin na arewa maso gabas.

Saurari rahoto cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Sojojin Najeriya Sun Ceto Wasu Mutane Daga Hannun 'Yan Boko Haram