SUDAN: Sojojin Kasar Sun Rutsa da Fararen Hula a Dafur

Shugaban Sudan Omar al-Bashir

Matakin soja da gwamnatin Sudan ta dauka akan Dafur ya kawo muguwar illa ga fararen hula

Wani babban jami’in kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya yace tunanin cimma yarjejeniya a yankin Darfur na kasar Sudan da yaki ya daidaita almara ce kawai.

Mataimakin babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da harkokin kiyaye zaman lafiya Edmond Mulet ya shaidawa Kwamitin sulhu na majalisar a birnin New York jiya Laraba cewa, matakin sojin da gwamnatin Sudan ta dauka kan ‘yan tawaye a Darfur ya rutsa da fararen hula da dama.

Mulet yace fadan ya sa kimanin mutane dubu saba’in da takwas kauracewa gidajensu bana, yayinda wadansu rahotanni ke nuni da cewa, mutane dubu 130 suka rasa matsugunansu.

Yace hare haren da ake kaiwa jami’an kiyaye zaman lafiya da ma’aikatan jinkai suna kawo cikas ga yunkurin taimakawa ‘yan gudun hijiran. Mulet ya kuma ce, akwai rahotannin dake nuni da cewa, ana kaiwa farin kaya hare hare, yayinda ake keta wadansu dokokin kare hakin bil’adama na kasa da kasa. Sai dai yace, jami’an kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya sun shawo kan hare haren da ake kaiwa farin kaya ta wajen shata iyakokin kariya, da kuma yin rangadi a kauyuka.

A cikin makon nan, kwamitin sulhu zai kara wa’adin aikin kiyaye zaman lafiya a Dafur da shekara daya