Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Kunar Bakin Wake A Masar Ya Kashe Mutane Hudu

Egyptian policemen secure Egypt’s national police academy, where an Egyptian criminal court sentenced ousted Islamist President Mohammed Morsi and 12 Brotherhood leaders and Islamist supporters to 20 years in prison over the killing of protesters in 2012,

Wani dan kunar bakin wake, ya ta da wani bam a wajen wasu masu ibadar gargajiya da ke kudancin kasar Masar, lamarin da ya raunata mutane hudu.

Jami’an kasar sun ce harin ya kai ga ‘yan sanda, sun harbe wasu mutane biyu, sannan dukkanin wadanda suka raunata babu masu yawan shakatawa a cikinsu.

Wajen Ibadan, wanda ke birnin Luxor, na daya daga cikin wuraren da hukumar adana tarihi ta Majalisar Dinkin Duniya ta UNESCO ta ware, wanda wuri ne da ke jan hankulan masu yawan shakatawa na ciki da wajen kasar ta Masar.

Ya zuwa yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai wannan hari.

A ‘yan shekarun nan, masu kaifin kishin Islama, sun sha kai hare-haren bindiga da na bama-bamai a yankin Sinai da ke Masar, inda suka fi mai da hankali kan jami’an tsaro

Wadannan hare-hare, sun yi kamari ne, tun bayan da babban hafsan sojin kasar kuma shugaba mai ci a yanzu, Abdel Fatah Al Sisi, ya jagoranci hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Muhammed Morsi a shekarar 2013.

XS
SM
MD
LG