Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Jinkirta Zaben Kasar Burundi


Shugaban kasar Burundi ya ce za a jinkirta zaben shugaban kasar, bayan makwanni da aka kwashe ana zanga zanga, tun bayan da ya ayyana cewa zai tsaya neman takara a wa’adi na uku.

A yau laraba, Shugaba Pierre Nkurunziza ya fitar da wata doka, wadda ta matsar da zaben shugaban kasar daga ranar 26 ga watan Yuni zuwa 15 ga watan Yuli.

Har ila yau shugaban ya matsar da zaben ‘yan majalisar kasar hare da na dattawa.

Shugabannin kasashen gabashin Afrika da Majalisar Dinkin Duniya ne suka nemi Nkurunziza da ya matsar da zabukan, domin a samu damar dakile boren da kasar ke fama da shi.

Zanga zangar dai ta barke ne tun bayan da Nkurunziza ya ayyana cewa zai tsaya takara a zabe mai zuwa, wanda ‘yan adawa suka ce ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar, da ya ba da damar yin wa’adi biyu.

Sai dai masu goyon bayansa sun ce, hakan bai sabawa kundin tsarin mulkin kasar ba, domin ‘yan majalisu ne suka zabe shi wa’adinsa na farko.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG