Tallafin Da Amurka Ke Baiwa Masar Na Cikin Wani Hali

Kwamitin da ke duba dangantakar Amurka da Masar.

Kwamitin kwararrun manazarta na dukkanin jam’iyyun Amurka biyu, kan dangantakar Masar da Amurka, sun bukaci Majalisar Tarayyar Amurka da ta sake tunani kan taimakon Dala Biliyan 1.5 da ake baiwa Masar, a dai dai lokacin da kasar ta ‘kasa shawo kan matsalar cin zarafin bil Adama.

Kwararrun sun nuna cewa karkashin shugabancin Abdel-Fattah el-Sissi sojojin Masar basa mutunta hakkin bil Adama, haka kuma gwamnatin ‘kasar na taimakawa wajen yada akidar ‘kin jinin Amurka.

‘Yan kwamitin dai sun gabatar da wannan bukata ne a wajen taron kwamitin na baya-bayan nan.

Michele Dunne, Daraktar shirye-shirye kan Gabas ta Tsakiya a kungiyar samar da zaman lafiya ta ‘kasa da ‘kasa, ta fara jawabinta ne da bayanin wani hoton bidiyon da ke nuna sojojojin Masar na kashe wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne a yankin Sinai.

Ta kuma yabawa shugaban ‘kasar Donald Trump, kan yadda bai damu ba wajen baiwa Masar duk abin da take so. Lokacin da shugaban Masar ya kawo ziyarar sa ta baya-bayan nan, gwamnatin Amurka ba ta yi alkawarin ci gaba da baiwa Masar tallafi ba tare da duba yadda halin da kasar ke ciki ba a cewar Dunne.