Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amfani Da Takunkumin Karya Tattalin Arziki Ga Koriya Ta Arewa


Daya daga cikin sakonnin dake fitowa karara sakamakon ganawar da shugaba Donald Trump da ‘yan majalissar kasar akan Koriya ta Arewa, shine sake nanata muhimmancin yin amfani da takunkumin karya tattalin arziki da bin hanyar diplomasiyya don matsa ma Koriya Ta Arewa lamba ta koma kan teburin sasantawa.

Yayin da ake ganin babu tabbas ga komawa bisa teburin sasantawar, kwararru na ganin goyon bayan China akan wannan kokari yana da muhimmanci. To sai dai kuma abin tambaya anan shine, ko China za ta goyi bayan matakan da ake shirin ‘daukawa kan Koriya ta Arewar.

Kwararru a China sun ce gwamnatin kasar na iya bakin kokarinta don ganin ta taka wa Koriya arewa burki. A farkon shekarar nan China ta rage yawan gawayin Kwal da ake shigowa da shi kasar daga Koriya ta Arewa, haka kuna ta kara tsuke hanyoyin hada-hadar kudade zuwa Koriya ta Arewar.

Lu Chao, dake zaman wani babban malami ‘dan asalin Koriya ta Arewa, da yanzu haka ke koyarwa a wata makarantar kimiyya dake Arewa maso Gabashin China, ya ce duk bankunan kasar China sun dakatar da harkokinsu da bankunan Koriya ta Arewa.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG