Tsohon Dan Wasa Ya Lashe Zabe A Pakistan

Imran Khan

Hukumar zaben kasar Pakistan ta bayyana wani tsohon jarumin wasannin motsa jiki da ya shiga siyasa Imran Khan a matsayin wanda ya lashe zaben majalisar amman kuma jam'iyyar sa ta kasa samun isassun kuri'un da suka fi kowanne don haka dole a kafa gwamnatin hadin gwiwa.


Sanarwar tana zuwa ne sa'oi kadan bayan da Khan ya bayyana jam'iyyar sa ta Tahreek-e-insaf a matsayin wacce ta lashe zaben jiya Alhamis. A wani jawabin samun nasara da ya yi ta kafar talabijin, yayi alkawarin magance matsalar talauci da cin hanci da rashawa dake addabar su ta hanyar sabon tsarin mulki a kasar.


Khan ya bada bayanin a lokacin da aka fitar da sakamakon kimanin kashi 90 cikin 100 na kuri'in zaben 'yan majalisar da aka gudanar ranar Laraba, inda jam'iyyar sa ta kere wa ta abokan adawar sa ta tsohon daurarren Firayim Ministan kasar Nawaz Sharif.
Kusan duk manyan jam'iyyun adawar sunyi zargin cewa an yi magudin zaben ne domin Khan ya samu nasara abinda hukumar zaben Pakistan ta musanta.


Shugaban hukumar zaben Sardar Mohammed Raza ya tabbatar da sahihancin zaben.