Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Facebook Ya Tafka Asarar Kimanin Dala Biliyan Dari Da Ishirin


Hannun jarin kamfanin facebook ya yi irin faduwar hannun jarin da ba a taba gani ba a tarihin hada hadar hannayen jarin kamfanin.

Kamfanin ya yi asarar kashi digo hamsin da bakwai cikin dari, watau 0.57% a daidai lokacin da aka rufe kasuwar hada hadar hannayen jari ranar Laraba, ya kasance asara mafi girma da aka taba samu a rana daya a harkar hada hadar hanayen jarin kamfanin.

Jiya alhamis hannun jarin kamfanin ya fadi da kashi goma sha tara cikin dari, inda aka sayar da shi a kan $176.26, abinda ya sa masu hannayen jari a kamfanin asarar duk ribar da suka samu a shekara ta dubu biyu da goma sha takwas, ya kuma janyo asarar kimanin dala biliyna dari da ishirin.

A jiya ne dai kamfanin ya sanar da amincewa da yin Karin kudin tsaron iyalin shugaban kamfanin Mark Zuckerberg daga dala miyan bakwai da dubu dari uku da aka kashe bara zuwa dala miliyan goma. Sabon Karin ya nuna kamfanin zai kashe kimanin dala dubu ishirin da bakwai kan tsaron shugaban kamfanin kowacce rana. Kamfanin ya kashe dala miliyan biyar da dubu dari takwas kan tsaron iyalin Zuckerberg a shekara ta dubu biyu da goma sha biyar.

Mujallar Sullicon Valley ta ambaci ta bakin hukumomin kamfanin cewa, kara kudin tsare iyalin Zuckerberg Alheri ne ga kamfanin, sakamakon barazanar tsaro da yake yawan samu.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG