Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MALAWI: Ana Yiwa Mata Masu Ciki Da Masu Jego Jinya Ta Wayar Tarho


Ester Terry tare da Khalifa a asibiti catania a kasar Italiya

Mata masu ciki da masu jego dake suke zaune a yankunan karkara a kasar Malawi suna samun taimakon ayyukan jinya ta hanyar aika sakon ko ta kwana kyauta ta wayar salula da ake kira “Chipatala pa Foni” ko kuma cibiyar lafiya ta wayar salula.

Shirin da wata kungiya mai zaman kanta da ake kira “VillageReach” take gudanarwa, yana hada mata dake zaune a yankunan karkara da jami’an jinya. Yanzu mata masu juna biyu da yawa suna samun kulawa daga lokacin da suke da ciki har zuwa haihuwa.

Shirin ya zama wata gada tsakanin wadanda ke zaune a nesa da asibitai da ma’aikatan jinya. Sai dai wannan ba cibiyar jinya bace, cibiya ce ta tuntubar mai jinya ta wayar tarho.

Ma’aikatan wannan cibiya sun sami horaswa a fannin kula da mata masu juna biyu, da kula da jarirai, da kula da lafiya kananan yara. Suna kuma amsa tambayoyi da bada shawarawari kan abinda ya shafi mata masu ciki da kuma masu jego.

Kasancewa sama da kashi saba’in cikin dari na al’ummar kasar Malawi suna zaune a yankunan karkara, da ratar a kalla kilomita ishirin da asibiti mafi kusa, gwamnati tana shirin sa wannan cibiyar tuntubar ma’aikatan jinya, a tsarin harkokin lafiyarta cikin shekara guda.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG