Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa Ya Rasu

Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa

Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa wanda ya rasu ranar Laraba 11 ga watan nan na Nuwamba yana da shekaru 84, a shekarar 1979 aka zabe shi a matsayin gwamnan jihar Kaduna amma daga baya aka tsige shi daga mukamin.

Marigayi Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa wanda aka haifa ranar 21 ga watan Agusta na shekarar 1936, shi ne gwamnan farar hula na farko a jihar Kaduna a jamhuriya ta biyu a Nijeriya kafin a tsige shi a ranar 23 ga Yuni na shekarar 1981.

A ranar Larabar nan ne aka yi jana’izar marigayi Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa a masallacin Sultan Bello da ke unguwar Sarki a Kaduna.

Marigayi Abdulkadir ya taba zama shugaban gamayyar jam'iyyun siyasar Najeriya ta CNPP, wato gamayyar jam'iyyun adawa a jamhuriya ta hudu.

Kafin rasuwarsa, ya kasance shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar Redemption Party (PRP) kuma ita ce jam'iyyar da ya tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2003.