Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Keta Hakkin Bil Adama A Najeriya


Shuwagabanin zanga-zangar Chibok da Manyan jami’an sojojin Najeriya a Abuja, 6 ga watan Mayu 2014.

Gwamnatin Najeriya na fuskantar matsin lamba da ta gudanar da bincike kan zarge-zargen da Kungiyar kare rajin bil Adama ta Amnesty International tayi cewa sojojin kasar sun yiwa fararen hula kisan gilla a yankin arewa maso gabashin kasar.

Kwarerran lawyan tsarin mulki a Najeriya kuma ‘dan rajin kare hakkin bil Adama BaristaYakubu Sale Bawa, na daga cikin mutanen dake kan gaba wajen matsawa gwamnati lamba sai ta gudanar da bincike. Inda yace, “Amnesty International kungiya ce ta duniya, wadanda suka shahara kan bincike saboda haka su ganau ne ba jiyau ba, bazasu zauna haka kawai su kirkiro labari hakanan akwai da akwai dalilin dayasa suka fitar da shi, kuma dolene ya kamata a duba.”

Shima gwamnan farko na farar hula a jihar Kaduna Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa yace tabbas a kwai bukatar yin wannan bincike, inda ya bayyana cewa bai kamata ba ace anyi watsi da wannan maganar ba saboda akwai kanshin gaskiya a cikin ta na cewa ana aikata hakan.

A jihohin Borno da Yobe akwai guraren da sojoji ke tsare mutane wanda alokata da dama kan hada da marasa laifi da ake gana musu azaba mai radadi wani lokacin ma harda kisa, A Damatirun jihar Yobe wasu shedar gani da ido sun gaya wakilin Muryar Amurka Hassan Maina Kaina cewa akwai wani guri da ake kira gwantanamo be da kuma masaukin shugaban kasa, yayin da a Maiduguri kuma kowa yasan barikin sojoji mai suna Giwa Barrack.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG