Tsohon Shugaban Kamfanin Nissan Ya Tsere Zuwa Lebanon

Tsohon Shugaban Kamfanin Nissan Carlos Ghosn

Tsohon Shugaban Kamfanin kera motocin Nissan, Carlos Ghosn, ya fada yau Talata, cewa, ya tafi Lebanon don guje ma abin da ya kira, "rashin adalci da bita da kullin siyasa" a Japan, inda yake fuskantar, tuhume-tuhume da yawa, na almundahanar kudi.

Tsohon Shugaban Kamfanin Nissan Ya Tsere Zuwa Lebanon

"Yanzu a Lebanon na ke, kuma ba za a sake tsare ni, a murdadden tsarin shari'ar Japan ba, inda ake ayyana laifi bisa hasashe, ake yawan nuna banbanci, ake kuma danne hakkokin bil'adama, wanda hakan, ya yi matukar saba ma nauyin, da ya rataye a wuyar Japan, a karkashin dokar kasa da kasa, da kuma yarjajjeniyoyin, da ya kamata, ta mutunta,” in ji shi.

An sha kama Ghosn, tun bayan da aka fara tsare shi, a watan Nuwamban 2018, amma aka sake shi, kan beli. Ko da aka sake shi, an bukaci, ya ci gaba da zama a Japan, kuma a cikin sanarwarsa, ba ta yi bayanin yadda ya bar kasar ba.

Lauyan Tsohon Shugaban Kamfanin Nissan Carlos Ghosn

Ghosn dan ƙasar Faransa, Brazil da Lebanon ne. Lauyansa, Junichiro Hironaka, ya fada wa manema labarai, a yau Talata, cewa, har yanzu, lauyoyinsa, na shari'a, su na rike da dukkan fasfo din Ghosn, kuma ya yi mamakin ficewar Ghosn.

Ghosn ya musanta zargin da ake masa.