Tukuicin Naira Miliyan 50 Saboda Daliban da Aka Sace

Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima.

Gwamnatin jihar Borno ta ce zata bayar da tukuicin Naira miliyan 50 ga duk wanda ya taimaka aka samo dalibai mata su kusan 200 da aka sace su daga Makarantar Sakandaren garin Cibok.

Gwamnan jihar Kashim Shettima, shine ya bayyana wannan a ganawar da yayi da manema labarai a birnin Maiduguri.

Mr. Shettima ya bayana cewa wannan lamarin abun bakin ciki ne, da kuma takaici. Gwamnan ya kara da cewa bai tabbatar da jimlar adadin yaran da aka sace.

A halin yanzu dai, 14 daga cikin wadannan dalibai sun samu damar kwacewa daga hannun wadanda suka sace su, kuma sun komo gidajensu.

Bayannan da daliban da suka tsere suka bayar, sun bayanna cewa ‘yan bindigar sun saka matan ne yi musu girki.

Jami’an makarantar sun bude rijista domin sanin wadanni yaran ne aka sace, kuma ya zuwa yanzu iyaye su wajen 50 sun bayanna cewa ‘ya’yansu na wannan makaranta, kuma suna cikin wadanda ‘yan bindigan suka sace ba’a san inda suka ba har yanzu.

Your browser doesn’t support HTML5

Tukuicin Naira Miliyan 50 Saboda Dalibai da Aka Sace - 2'01"