UEFA: City Ta Dauki Hanyar Zuwa Semi-Final Bayan Doke Bayern 3-0

Haaland bayan da ya zura kwallo a ragar Bayern

Real Madrid ce ta cire City a zagayen semi-finals a kakar wasa ta bara a gasar ta Champions League.

Manchester City ta kasar Ingila ta fara jin kamshin zagayen Semi-Final a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai ta Champions League bayan da ta lallasa Bayern Munich da ci 3-0

Kwalleyen Rodri, Bernardo Silva da Erling Haaland ne suka ba City wannan nasara a karawar ta quarter-final a filin wasa na Etihad.

Bayern ta je wannan wasa ne da kwarin gwiwar samun nasara, bayan da ta doke Inter Milan, Barcelona da Paris Saint Germain.

Amma duk da sabon kwacinsu Thomas Tuchel, Bayern ta gaza gano bakin zaren lallasa City.

Chelsea ce ta doke City a wasan karshe na Champions League a shekarar 2021 a lokacin Tuchel na horar da Chelsea.

Real Madrid ce ta cire City a zagayen semi-finals a kakar wasa ta bara a gasar ta Champions League.