Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Raheem Sterling Zai Koma Chelsea

Dan wasan Manchester City, Raheem Sterling
Dan wasan Manchester City, Raheem Sterling

Ana fatan za a kammala cinikin dan wasan gabanin kungiyar ta Chelsea ta fara rangadin wasannin ta da tsimi da za ta yi a kasar Amurka kafin a fara sabuwar kakar wasa.

Chelsea ta cin ma matsaya kan kudin da za ta sayi dan wasan abokiyar hamayyarta Manchester City, Raheem Sterling.

Kungiyar ta tanadi kudi har dalar Amurka miliyan 60 kan dan wasan mai shekaru 27 bisa kwantiragin shekaru biyar a Stamford Bridge kamar yadda kamfanin daillancin labarai na AP ya ruwaito.

Ana fatan za a kammala cinikin dan wasan gabanin kungiyar ta Chelsea ta fara rangadin wasannin ta da tsimi da za ta yi a kasar Amurka kafin a fara sabuwar kakar wasa.

Sterling ya zura kwallaye 13 a wasannin gasar Premier Leage 30 da ya bugawa Manchester City a kakar wasan da ta shude.

Ya kuma samu nasarar lashe kofin gasar ta Premier League sau hudu tare da City.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG