VOA Da USAID Sun Yi Taron Kiwon Lafiya A Bauchi

Lange-lange mai ramar keta, sauro kenan mai yada cutar maleriya

Muryar Amurka da Hukumar raya kasashe masu tasowa ta Amurka sun kaddamar da shirin yaki da zazzabin cizon sauro a jahar Bauchi
Gidan Rediyon Muryar Amurka, VOA da Hukumar raya kasashe masu tasowa ta Amurka, USAID, sun kaddamar da wani gagarumin gangamin hadin guiwa na yaki da masassarar cizon sauro a garin Bauchi. Taron kaddamar da shirin ya samu halartar wasu jami’ai daga hukumar kula da lafiya matakin farko ta jahar Bauchi da kuma wasu kwararru daga hukumar BAKATMA mai yaki da cutar kanjamau da tarin fuka da masassarar cizon sabro a jahar Bauchi. A cikin rahoton da wakilin Sashen Hausa Nasiru Yakubu Birnin Yero ya aiko ma na daga Bauchi ,Alhaji Umar Babuga Abubakar na hukumar BAKATMA ne ya fara yiwa taron tambihi game da wuraren da sauro yake zama ya na hayayyafa.

Your browser doesn’t support HTML5

VOA da USAID sun kaddamar da shirin yaki da maleriya a Bauchi - 2:00


Shi ma abokin aikin mu Ibrahim Alfa Ahmed wanda ya jagoranci tawagar wakilan Muryar Amurka a wajen taron na Bauchi, ya shaidawa mahalarta cewa Gidan rediyon Muryar Amurka, VOA da hukumar raya kasashe masu tasowa ta Amurka, USAID, sun kirkiro da wannan shiri ne domin fadakar da al’umma game da yadda za a kare kai daga kamuwa da cutar masassarar cizon sauro.

Ma'aikacin Sashen Hausa na VOA Ibrahim Alfa Ahmed jagoran babban taron na yaki da maleriya a Bauchi


Haka nan su ma wasu matasa su kimanin dubu daya da dari biyar magoya bayan kungiyar wasan kwallon kafar Muryar Amurka ta VOA Flamingos ta garin Bauchi ba a bar su a baya ba, daga wajen taron sai suka shiga aikin sare ciyawa da yasar wani magudanin ruwa mai tsawon kimanin mita dubu biyar da dari biyar dake fadamar mada a titin Mohammed Namadi Sambo a garin Bauchi.