Accessibility links

Muhimman Bayanai Kan Rigakafi Da Kula Da Kananan Yara


Wadansu yara suna jira a yi masu rigakafi

Masana sun bayyana cewa, ana fara kulawa da lafiyar kananan yara ne daga ranar da mace ta sani cewa ta dauki ciki har zuwa lokacin da suka cika shekaru biyu, domin kare shi daga kamuwa da cututuka bayan ya girmai

Masana sun bayyana cewa, ana fara kulawa da lafiyar kananan yara ne daga ranar da mace ta sani cewa ta dauki ciki har zuwa lokacin da suka cika shekaru biyu, lokacin da idan an bi dukan dokokin rigakafi da shayar da yaro da nonon uwa, to ya kamata yaro ya sami dukan alluran rigakafin da yake bukata da zasu kare shi dukan rayuwarshi. A wannan lokacin ya wuce hatsarin kamuwa da cututukan dake kashe kananan yara abinda zai taimakesu su gima cikin koshin lafiya.

Kwararru sun bayyana cewa, kwanaki dubu daya na farko a rayuwar kananan yara tana da amfani matukaa rayuwarsu. Wadannan kwanaki 1,000 sun hada da wata tara da jariri yake a cikin ciki da kuma shekaru biyu na farkon rayuwar sa a duniya. Masu bincike sun ba da shawara cewa da zara mace ta gane cewa tana da ciki, sai ta koye halin tsabta da zai taimake ta da kuma dan da ke cikin mahaifan ta.

Wani binciken da Prof. David Barker da kungiyarsa suka yi a babbar Jami`ar Southampton, ya nuna cewa lokacin zaman jariri a mahaifa na iya shafar komai-daga tushen samin ciwon suga ko kuma ciwon zuciya sa`ad da ya tsufa, da lafiyan jikinshi da kuma tsawon rayuwarshi.

Masu binciken sun gano cewa abincin da uwa mai ciki ke ci zai iya kan shafar lafiyar jariri da cikin mahaifa da kuma yadda mahaifar ke aiki, sannan mummunar rayuwa kamar shan taba, kwayoyi da giya kuma kan zama da hatsari ga lafiyar jaririn.

Malaman kimiyya sun bayyana cewa yana yiwuwa rashin lafiyar da mai ciki take fama dashi ya shafi lafiyar jariri, kamar yadda ya kan iya shafar kayan cikin jariri kamar cututtuka kamar ciwon suga a rayuwa ta gaba. Sun kuma ce jariran da aka haifa da nauyinsu bai kai yadda ya kamata ba suna da hatsarin fama da ciwon zuciya a duk tsawon rayuwar.

Likitoci sun bayyana cewa, kananan yara suna iya samun kariya daga cututukan da zasu iya dauka daga iyaye ko wadansu manya idan aka yi masu allurar rigakafi tare da shayar da su da nonon uwa kadai a farkon wata shida na rayuwa domin su iya samun mayakan cututuka masu karfi a cikin jininsu da zasu rika yaki da cututtuka, a kwai rigakafi da dole ne yaro ya samu har sai ya kai shekaru biyar.

Cututukan dake kashe kananan yaran da ake bukatar yi masu rigakafi suna hada da ciwon hakarkari, ciwon inna, cutar fuka, ciwon tari, bakon dauro, ciwon rinku da ciwon makarau.
XS
SM
MD
LG