Wani Dalibi Ya Harbe Mutane 19 a Rasha

Wani dalibi mai shekaru 18 ya harbe ya kashe mutane 19 kana ya jikata sama da wasu hamsin a wata kwalejin kere kere a Crimea.

‘Yan sanda sun ce Vladislay Roslyakov ne ya yi harbin, dalibin ajin karshe a kwalejin dake birnin Black Sea a yankin Kerch na Crimea.

Masu bincike da darekatan kwalejin sun fada cewa, bayan wata fashewa, sai wani dan bindiga ya shiga ginin makarantar ya fara harbin kan mai uwa ba wabi a Kwalejin kere kere a yankin Kerch.

Dmitry Peskov, shine mai magana da yawun shugaban Rasha, yace Vladmir Putin ya bada umarnin gudanar da binciken kwakwaf a kan wannan batu kana ya aike da ta’aziyarsa ga iyalan wadanda abin ya shafa.