Majalisar Dattijai Da Ta Wakilai Sun Daidaita A Kan Sabon Tsarin Zabe A Najeriya

Majalisar dattijan Najeriya ta yi na'am da kudurin da majalisar wakilan kasar ta dauka tun da fari na sauya tsarin yadda za a gudanar da manyan zabubbuka masu zuwa a kasar, a bayan da wani kwamitin hadin guiwa na daidaita kudurin doka na majalisun biyu yayi na'am da wannan matakin.

Sanata Sulaiman Nazif, shugaban kwamitin kula da harkokin zabe a majalisar dattijai, yace sun cimma daidaito a kan cewa a yanzu tsarin da za a bi a zabubbukan masu zuwa, shine za a fara yi ne da zaben 'yan majalisun tarayya biyu, watau majalisar dattijai da ta wakilai, sannan sai a gudanar da zaben 'yan majalisun dokokin jihohi da gwamnoni, a karshe kuma a gudanar da zaben shugaban kasa.

Yace a yanzu, zasu tura wannan kuduri ma shugaba Muhammadu Buhari, wanda tilas sai ya rattaba hannu a kai kafin ta zamo doka.

Sai dai kuma wani dan majalisar wakilan tarayya, Ahmed Babba Kaita, ya bayyana wannan matakin da cewa na yaudara ne kawai. Ya fadawa wakiliyar Muryar Amurka Medina Dauda, cewa, "wannan sauyi da aka yi na zaben shugaban kasa, siyasa ce. Ana nema a cimma wata manufa ce ta yadda wadanda ba su taka rawar gani ba a cikin jam'iyyar adawa, zasu iya samun gurbi in sun fita daga cikin jam'iyyar."

Wakilin yace makasudin sauya tsarin zaben shine a namemi yadda za a fasa jam'iyya mai mulki ta APC.

Shi kuma shugaban Cibiyar Nazarin Al'amuran Ci Gaba ta Kukah, Bishop Mathew Hassan Kukah, yace akwai abubuwan koma-baya da yawa a harkar dimokuradiyyar Najeriya, wadanda kuma ke tayar masa da hankali.

Ga cikakken rahoton Medina Dauda...

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar Dattijai Ta Bi Sahun Ta Wakilai Wajen Amincewa Da Sauya Tsarin Zabe A Najeriya - 2'57"