Wasu 'Yan Bindiga da Ba'a Saniba Sun Fasa Gidan Yarin Garin Minna

Gidan Yarin Birnin Minna.

Wasu 'yan bindiga da ba a sani ba sun fasa gidan yarin garin Minna.

Da misalin karfe shida da rabi agogon Najeriya 6:30 wasu 'yan bindiga da ba a san ko suwaye ba, suka fasa gidan yarin Minna a jihar Naija. Kuma dai rahotanni na nuna cewar kimanin fursinoni dari biyar ne ke gidan,( 500) wasu daga cikinsu sun gudu. Amma wasu rahotanni sun ce ba'a sami hasarar rayuka ba zuwa yanzu.

Ta bakin jami’in yada labarai na gidan yarin Mal. Rabi’u Sha’aibu da ke Minna, yace zuwa yanzu ba bu rahoton ko mutun nawa ne suka gudu, da kuma adadin wanda suka jikkata. Ya kuma kara da cewar babu tabbacin suwanene suka kai wannan harin, an kai mutun daya asibiti.

Yanzu haka dai anfara kamo wasu daga cikin fursinoni da suka gudu. Haka ma dai al'umar wannan yanki sunacikin damuwa, don jami'an tsaro sun hana shiga da fita cikin unguwar da abun ya faru. Babu wata harka da ke gudana a ciki da kewayen gudan yarin.