Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yanbindiga Sun Kai Hari a Ashaka da Bajoga cikin Jihar Gombe


Ibrahim Hassan Dankwambo, gwamnan jihar Gombe

'Yan yakin sa kai sun sake kai hari a Ashaka karo na biyu cikin watanni biyu

Rahotanin dake fitowa daga Nigeria na cewa 'yan yakin sa kai a jihar Gombe, arewa maso gabashin kasar, sun kai hari kamfanin siminti na Ashaka. Shine hari na biyu da aka kai kamfanin cikin watanni biyu.

Rahotannin sun baiyana cewa yan yakin sa kai dauke da bindigogi sun kutsa cikin kamfanin siminti Ashaka dake kusa da garin Bajoga da karfin tsiya da sanyin safiya jiya Alhamis. Ba'a tantance yawan mutanen da suka jikatta ba.

Shedun gani da ido sun fadawa 'yan jarida cewa haka kuma yan bindiga sun kai hari birnin suka yi ta harbi jefi jefi, to amma da alama sun auna kamfanin simintin ne mallakar wata kungiyar kasar Faransa

Jami'an yankin sunce mutane sun fice daga kamfanin kafin a kai harin.

A watan jiya na Nuwamba an kai samame kamfanin lokacinda ‘yan bindiga suka yi awon gaba da motoci da kuma karikitan harhada nakiyoyi

XS
SM
MD
LG