Ya Kamata Mu Koyi Kyawawan Dabi'un Shaikh Usman Sharubutu Na Kulla Kyakkyawar Alaka Tsakanin Addinai-Mahalarta

Imam of Ghana visited by Christians Pastors

Shugabannin Musulmi sun gargadi mahalarta wani taron bude masallaci da makaranta a birnin Accra da su kasance masu neman zaman lafiya da hadin kai tsakanin addinai dake makwabtaka da juna a kasashen mu na Afrika ta Yamma da don ci gaban al’ummar mu.

An yi wannan kira ne a wurin bude masallaci da makarantar haddar Alkur’ani da babban limamin kasar Ghana Dakta Shaikh Nuhu Usman Sharubutu ya gina a unguwar Joma dake karamar hukumar Ablekuma a birnin Accra.

Taron buden masallacin da aka yi a daidai sallar Juma’a ya tattaro mahalarta daga kasashen Afrika ta Yamma, da suka hada da babban Khalifan Sheikh Ibrahim Kaula kuma shugaban Faila na duniya Shaikh Mahey Ibrahima Niyass daga Senegal, Khalifan Shehu Ibrahima Niyass na Najeriya mai martaba Malam Muhammadu Sanusi Lamido na biyu, babban limamin masallacin birnin Abuja, Farfesa Ibrahim Makari da sauransu.

Imam of Ghana

Babban bako a wurin taron mataimakin shugaban kasar Ghana, Dakta Mahmud Bawumia, ya kwatanta Shaikh Usman Nuhu Sharubutu da babbar kyauta da Allah Ya yi wa Ghana saboda irin gudunmuwar da yake bayarwa ga ci gaban kasa da kuma kawo hadin kan kasa.

Farfesa Ibrahim Makari, wanda ya yi jawabinsa a cikin harshen larabci, ya ce “lallai al’ummar Musulmai na bukatar su amfana da hikimar wannan jagora Shaikh Usman Nuhu Sharubutu, wajen tabbatar da zaman lafiya tsakanin al’ummar Musulmi da abokan zamansu da ba Musulmai ba”.

Vice President of Ghana Dr. Bawumia, Sanusi Lamido and Baba Addini of Ghana

A cikin takaitaccen jawabin da ya yi, mai martaba Khalifa Malam Sanusi Lamido Sanusi na biyu, ya jaddada kalaman Farfesa Makari inda ya ce idan sauran kasashen Afrika zasu yi koyi babban limamin Ghana wurin kyakkyawar alaka da zamantakewa tsakanin al’umma zai taimaka ainun.

Yace, “Allah Yasa sauran shugabanni a kasashen Afrika su bi sawunsa, kana su koyi muhimmancin zaman tare cikin lumana don ci gaban nahiyar mu”.

Wasu mahalarta kuma sun bayyan farin cikin su da wannan aikin da limamin limaman Ghana Sheikh Usman Nuhu Sharubutu ya yi.

Ga dai rahoton Idris Abdullah Bako daga birnin Accra:

Your browser doesn’t support HTML5

Ya Kamata Mu Koyi Kyawawan Dabi'un Shaikh Usman Sharubutu Na Kulla Kyakkyawar Alaka Tsakanin Addinai-Mahalarta.MP3