Yadda Nasarar Kamaru a Kan Comoros Ta Zo Da Rashi

Your browser doesn’t support HTML5

Mutune da Yawa Sun Rasa Rayukansu Bayan an Kammala Wasa Tsakanin Kamaru da Comoros

Mutune da yawa sun rasa rayukansu bayan an kammala wasa tsakanin Kamaru da Comoros a ranar Litinin da yamma. Kamaru ta yi nasara kan Comoros, amma nasarar mai ɗaci.

À ƙarshen wasa tsakanin Kamaru da Comoros, mutun 8 daga cikin' yan kallo sun rasa rayukan su, inda wasu da dama suka jikkata a sanadiyar cunkoso da aka samu wajen fitowa daga filin wasa.

Wadanda suka raunana, an kai su asibitin Messassi da ya fi kusa da filin wasan Olembe.

À fannin wasa, Kamaru ta tabbatar da kasancewar ta ɗaya daga cikin ƙasashen da ake yi wa zaton cin kofin Afirka na bana. Indomitables Lions sun doke Comoros ci 2-1.

Lamba 12 Kamaru mai suna Karl Toko Ekambi ne ya bude raga a mintuna 29 da fara wasa. Sa'annan Kaftan Vincent Aboubakarya wanda ya fi cin kwallaye ya zura ƙwallo daya a mintuna 70.

Duk da haka 'yan wasan Comoros ba su yi ƙasa a gwiwa ba. A mintuna 80, Youssouf M'Changama mai ɗauke da lamba 10 ya zura kyakkyawan ƙwallo a bugun daga kai sai mai tsaron gida. Amma hakan bai hana yan Kamaru zuwa kwata fainal ba, inda za su keta raini da Gambiya a ranar Asabar mai zuwa a birnin Douala.

Abin sani anan shi ne 'yan Comoros sun ƙarasa wannan wasa da mutun goma mai makon 11 a sanadiyar jan kati da aka bai wa Nadjim Abdou, a mintuna 7 da fara wasa.