Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Kallo Shida Sun Mutu A Wasan Da Kamaru Ta Doke Comoros


'Yan wasan Kamaru Vincent Aboubakar da Michael Ngadeu-Ngadjui suna murnar zura kwallo a ragar Comoros

Wasu shaidu sun ce lamarin ya rutsa har da yara kanana da dama.

Akalla mutum shida suka mutu a wani turmutsutsi da ya faru a filin wasan Olembe da ke birnin Yaounde a kasar Kamaru.

Lamarin ya faru ne a kofar shiga filin wasan, yayin da Kamaru da ke karbar bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afirka ta AFCON take karawa da Comoros a zagayen ‘yan 16.

Wasu da suka shaida lamarin sun ce al’amarin ya faru ne a lokacin da masu kula da kofar filin wasan suka rufe kyauran filin.

Gwamnan yankin Kamaru ta tsakiya Naseri Paul Biya, ya fadawa kamfanin dillancin labaran AP cewa ana fargabar adadin zai fi haka.

“Ba ma matsayin da za mu ba da adadin mutanen da suka mutu.” In ji Biya.

Jami’an asibitin Messassi sun ce sun karbi mutum 40 da suka ji raunuka daban-daban, amma ba duka marasa lafiyar suka iya ba kulawa ba.

“Wasu daga cikin mutanen da aka kawo asibitin suna cikin mawuyacin hali.” Oliga Prudence, daya daga cikin masu kula da marasa lafiya ta fadawa AP.

Wasu shaidu sun ce lamarin ya rutsa har da yara kanana da dama.

Jami’an wasan sun ce kusan mutum dubu 50 ne suka yi yunkurin shiga filin wasan mai daukan mutum dubu 60.

Bisa yadda aka tsara, kashi 80 cikin 100 na adadin mutane aka amince su shiga kallon wasan domin kaucewa yada cutar coronavirus.

Kamarun ta doke Comoros da ci 2-1, nasarar da ta ba ta damar tsallakawa zagayen quarter-finals.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG