Yajin Aikin Likitocin a Najeriya

Likitocin a dakin tiyata.

Yajin aikin Likitoci ya jefa harkokin kiwon Lafiyar cikin tagayyara.

Yajin aikin da kungiyar Likitocin keyi a Najeriya ya jefa harkokin kiwon lafiya cikin halin tagaiyara inda kananan jami’an kiwon lafiya ke kula da asibitocin.

Likitocin de da sa hannun shugaban kungiyarsu Dr. Kayode Obenbe, sun jera bukatu ashirin da hudu ne ga Gwamnati don a biya musu kafin su koma koma bakin aiki.

Zuwa yanzu de kokarin da muka yi domin jin ta bakin minister lafiya, Dr. Oyebuchi Chukwu, da karamin Minista, Dr. Haliru Alhassan, ya ci tura.

A Najeriya, dai ko Likitocin na aiki masu hannu da shuni kan je kasashen wajen ne kokuma su je Asibitici masu zaman kansu domin neman magani.

Ya zama mai mahimmanci Gwamnati ta shawo kan wannan lamarin don amfanin akasarin aluma.

Your browser doesn’t support HTML5

Yajin Aikin Likitoci - 2'40"