'Yan Bindiga Na Ci Gaba Da Tada Kayar Baya a Jihar Neja

A jihar Neja da ke Najeriya, 'yan bindiga masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa na ci gaba da cin karensu babu babbaka a yankunan kananan hukumomin Rafi da Shiroro a jihar.

Rahotanni a baya bayan nan sun tabbatar da cewa ya zuwa yanzu akwai garuruwa sama da 40 da tuni al'ummominsu suka tsere daga garuruwan saboda wannan matsala ta 'yan bindiga. Al'ummomin yankin dai sun ce maharan na yi masu kisan gilla tare da yi wa mata fyade da kuma sace dabbobi.

Wani Basaraken yankin Jibiril Abdullahi Alawa, ya tabbatar da cewa 'yan bindigar sun kashe mutane sosai kuma idan suka je wuri sukan yi ta harbi. Ya kara da cewa ko a kwanan nan sun kai hari a garin Farin Doki inda suka kashe mutum 4 suka kuma tafi da akalla mutum 9, a gundumar Galadiman Kogo .

Zagi Dabi, dake Zaman mataimakin shugaban wata kungiyar matasan 'yan kabilar Gwari da ya fito daga yankin na shiroro ya ce tabbas mutanensu duk sun tsere daga matsugunnansu domin neman tsira da rayukansu. Ya kara da cewa ba dare ba rana a ko da yaushe 'yan bindigar suka ga dama suna kai hari.

Ya zuwa yanzu dai akwai manoma da yawa ba zasu iya noma gonakinsu ba a wannan shekarar saboda yanayin tsaro a yankin na Shiroro mai madatsar ruwa, dake da daya daga cikin tashoshin samar da lantarki a Nigeria.

Mai bai wa gwamnan jihar Neja shawara akan sha'anin siyasa, Alhaji Umar Kolo, ya yi kira ga gwamnatin Nigeria da ta kai wa yankin dauki saboda fargaban fadawa yanayin karancin abinci nan gaba, bisa la'akari da yadda yankin yake bada gudummowa ta fuskar samar da abinci a kasar, ya ce ya kamata a maida hankali wajen samar da zaman lafiya.

Rundunar 'Yan sandan jihar Neja ta ce tana kokarin fatattakar 'yan ta'addan a wannan yanki. Ko da yake kwamishinan 'yan sandan jihar, Alhaji Adamu Usman ya ce suna neman hadin kan jama'a ta hanyar basu bayanai.

Ita ma gwamnatin jihar Neja ta ce tana shirin daukar mataki mai karfi akan wannan matsala. Gwamnan jihar, Alhaji Abubakar Sani Bello ya ce gwamnnati za ta dauki mataki ta yi abinda ya dace.

Ga karin bayani cikin sauki.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Bindiga Na Ci Gaba Da Tada Kayar Baya a Jihar Neja