Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 22 a Jihar Naija

Mazauna garin da Muryar Amurka ta yi hira da su sun bayyana cewa, i zuwa lokacin hirar, hukumomi basu riga sun isa inda lamarin ya faru ba, suka kuma ce gawarwakin ‘yan bangar suna daji ba ayi jana’izarsu ba.

A can garin Dukku dake yankin Karamar Hukumar Rijau kuwa, Maharan sun hallaka ‘yan banga 17 bayan wani dauki ba dadi da suka yi da su a lokacin da maharan suka yi yunkurin shiga garin na Dukku.

Mazauna garin da Muryar Amurka ta yi hira da su sun bayyana cewa, i zuwa lokacin hirar, hukumomi basu riga sun isa inda lamarin ya faru ba, suka kuma ce gawarwakin ‘yan bangar suna daji ba ayi jana’izarsu ba.

Duk Kokarin jin ta bakin Rundunar yan sandan jihar Nejan akan kannan al’amari da wakilinmu yayi, yaci tura domin kuwa kakakin yan sandan jihar, ASP Wasiu Abiodun bai dauki waya ba kuma bai maida martani sakon wayar hanu da aka aika mashi ba .

Sai dai gwamnatin jihar Nejan ta tabbatar da aukuwar wannan al’amari. Kwamishinan Labarai na jihar Nejan Alh.Sani Abubakar bayan jajantawa wadanda lamarin ya shafa yace, gwamnati na iya kokarinta wajan kawo karshen wannan tashin hankali.

Ya kara da cewa, “ saboda wadannan abubuwa da suka faru, yasa kowa cikin halin jimami. Akwai matakai da muka dauka na nan da nan da ba zamu bayyana ba saboda dalilan tsaro, yawanci idan aka bar shi a sirrance ya fi tasiri. Amma ina so in tabbatar wa al’umma cewa gwamnati ta dau matakai dai dai gwargwado.”

A halinda ake ciki dai, yanzu haka akwai gwamman mutane a garin na Kagara da wadan nan ‘yan bindiga suka yi awon gaba da su.

Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari:

Your browser doesn’t support HTML5

'yan bindiga sun kashe mutane 22 a Jihar Nejan Nigeria