‘Yan Bindiga Sun Sace Wani Basarake A Sakkwato

Yan bindiga.

A Najeriya, ganin yadda har yanzu jama'a ke fama da matsalolin rashin tsaro, ya sa wasu daga cikin jagororin al'ummomi ke dora alhakin cin zarafin da ake yi wa jama'a ga Shugabanni dake rike da madafun iko.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan bindiga ke ci gaba da gallaza wa jama'a yadda suke so, kamar yadda suka sace wani basarake da daren jiya Lahadi a Sakkwato.

‘Yan Najeriya na ci gaba da fuskantar barazanar ‘yan bindiga a sassa daban daban na kasar, abinda jama'ar ke ta mamakin yadda aka kyale barayin suna cin Karensu ba babbaka.

Jihar Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya na daga cikin jihohin da ayyukan ‘yan bindiga ke gudana babu kakkaubtawa, domin ko a daren jiya Ladahi sun yi awon gaba da basaraken garin Mammande, Umar Abubakar, dake cikin karamar hukumar Gwadabawa dake gabashin Sakkwato.

Ku Duba Wannan Ma SOKOTO: Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 20 A Wani Sabon Hari

Shugaban karamar hukumar ta Gwadabawa Aminu Aya ya ce da misalin karfe biyu na dare ne maharan suka zagaye gidan basaraken suka ce ya nuna musu gidajen masu kudi na garin.

Abinda ke kara daga hankalin mutanen yankin shi ne ganin yadda ‘yan bindigar suka mayar da garin madaddalarsu, acewar shugaban karamar hukumar.

Yankin Sabon Birni ma, har yanzu tsugune bata kare wa jama'ar yankin ba a cewar wani mazaunin garin, Tarah Hassan Tarah.

Na yi kokarin jin ta bakin rundunar 'yan sanda akan wadannan hare haren amma abin ya gagara.

Ku Duba Wannan Ma SOKOTO: Yan Bindiga Sun Sace Wani Dan Kasuwa Dan Kabilar Igbo Da Kuma Wani Hakimi

Ganin yadda gwamnati ke ko-oho da yadda jama'a ke fuskantar matsalolin rashin tsaro, duk da yake tana cewa tana kokarin magance matsalolin, ya sa wasu jagororin jama'a ke dora alhakin matsalolin ga shugabanni, kamar yadda Hon Aminu Almustapha Boza, dan majalisar jiha mai Wakiltar Sabon Birni ke cewa.

Lamarin rashin tsaro dai a Najeriya, a iya cewa, ya kule tunanin ‘yan kasa, wadanda sun yi ta kokawa, amma abin dai sai yadda Allah yayi.

Saurari rohoton Muhammad Nasir:

Your browser doesn’t support HTML5

‘Yan Bindiga Sun Sace Wani Basarake A Sakkwato