Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SOKOTO: Yan Bindiga Sun Sace Wani Dan Kasuwa Dan Kabilar Igbo Da Kuma Wani Hakimi


Wani dan bindiga
Wani dan bindiga

A Najeriya ayukkan ‘yan bindiga na ci gaba da fadada sannu a hankali zuwa sassa daban daban.

Abinda ke nuna hakan shi ne yadda 'yan bindigar suka kutso kai a mazabar gwamnan Sakkwato suka sace wani dan kasuwa dan kabilar Igbo da kuma wani hakimi.

A arewacin Najeriya da wuya a samu jiha daya da ‘yan bindiga basu shiga suka gallazawa jama'a ba, duk da ko kokarin da mahukunta ke cewa suna yi na dakile ayukkan ‘yan bindigar.

Jihar Sakkwato dake arewa maso yammacin kasar ta sha fama da matsalar ta ayukkan ta'addanci a gabashi da arewacin jihar kuma yanzu kudancin jihar ne ke sake fuskantar matsalolin bayan da aka samu saukin su a baya.

A daren lahadin wannan mako masu garkuwa da mutane sun kai hari gidan wani dan kasuwa dan kabilar Igbo mai suna Tony Umedezue dake zaune a garin Tambuwal Mahaifar gwamnan Sakkwato suka yi awon gaba da shi.

Daraktan sadarwa na mabiya darikar Catholic a Sakkwato Rev. Father Christopher Omotosho ne ya tabbatar da sace mutumin wanda yace wakilin majami'arsa ne. A hirar shi da Muryar Amurka ya bayyana cewa:

“Sun kai hari gidan ne suka fasa dakin da yake ciki suka shiga suka dauki mutumin, sun yi ta harbe-harbe a sassan gidan a tagogi a makewayi da sauransu, sun tafi da shi amma dai basu taba iyalinsa ba, matar sa da yara suna nan lafiya kalau.”

“Jami'an ‘yan sanda sun je gidan bayan gari ya waye, sun ma ga kwalfunan albarusai na harbe-harben da barayin suka yi, yanzu dai muna dakon muji kira daga barayin da suka sace mutumin”

Yankin Kebbi ma dake makwabtaka da Tambuwal da kuma jihohin Zamfara da Kebbi ya sake fuskantar matsalolin na rashin tsaro domin a cikin mako daya mahara sun afkawa garuruwa da dama a yankin, kamar yadda shugaban jam'iyar PDP mai mulkin jihar Sakkwato na karamar hukumar ya shedamin.

Muryar Amurka ta nemi ta ji ta bakin kakakin rundunar ‘yan sanda DSP Sanusi Abubakar akan wadannan hare haren na Tambuwal da Kebbe amma yunkurin ya ci tura.

Har-wa-yau maharan sun dawo garin Zugu suka sace wani karamin hakimi.

Masana lamurran tsaro dai sun jima suna bayar da shawarwari akan yadda ya kamata a tunkari matsalolin rashin tsaro da suka dabaibaiye Najeriya, sai dai su kuwa mahukuntan kasar suna cewa suna daukar matakai wadanda kawo yanzu sun kasa shawo kan matsalolin.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG