'Yan Demokrat Za Su Sanar Da Daftarin Tsige Trump

Shugaban Kasar Amurka Donald Trump

'Yan jam’iyyar Demokrat da ke jagorancin majalisar wakilan Amurka suna shirye shiryen sanar da daftarin dokar tsige shugaban Amurka Donald Trump da sanyin safiyar yau Talata.

Shugabar majalisar wakilan Amurka, Nancy Pelosi ta gana da shugabanin kwamitoci daban daban a jiya Litinin da daddare bayan da kwamitin shari’a ya kammala sauraron bahasin tsige shugaba Trump da shugaban kwamitin dan jam’iyyar Demokrat, Jerold Nedler, yake cewa yunkurin shugaba Donald Trump na yin magudi domin ya lashe zabe wata babbar barazana ce ga tsaron kasar mu.

Shugaban kwamitin harkokin waje na majalisar wakilan Amurkan Eliot Engel, ya fadawa manema labarai bayan da suka gama tattaunawa cewa, yana tunanin akwai yarjejeniyoyi da yawa. Kuma za ku ji wasu daga ciki gobe.

Dan majalisar bai bada wani Karin bayani ba a kan ko daftarin dokar tsige shugaba Trump nawa suka shirya amma ana tsammanin za su hada da yin amfani da karfin ikonsa ba bisa ka’ida ba da kuma yiwa yan majalisu Karen tsaye yayin da suke bincike.