Ana kyautata zaton Kwamitin Majalisar Wakilan Amurka kan bayanan sirri, yau dinnan Talata, zai gabatar ma jama'a sakamakon bincikensa da kuma matakan da ya bayar da shawarar a dauka a binciken yiwuwar tsige Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Kwamitin, Adam Schiff ya fada wa kafar labarai ta MSNBC a daren jiya Litinin cewa, kwamitin na kan kammala rahoton. Ya kuma ce kwamitin zai kada kuri'a da daren yau Talata kan batun mika rahoton a hukumance ga kwamitin shari'a, wanda mambobinsa za su yanke shawara kan ko za su rubuta takardar bukatar tsige Shugaba Trump ko a'a.
Kwamitin Shari’a na shirin fara nasa zaman sauraren ba'asin ranar Laraba, kuma za su yi hakan ba tare da lauyan Trump ya na wurin ba.
Shugaban ya ce ba zai tura wakilai ba "saboda gaba daya rudani ne."
Za ku iya son wannan ma
-
Janairu 19, 2021
Yau Jajibirin Rantsar Da Sabon Shugaban Amurka Joe Biden
-
Janairu 19, 2021
Tasirin Jihar Pennsylvania A Zaben Shugaban Kasar Amurka
-
Janairu 18, 2021
Joe Biden Na Shirin Gabatar Da Albishir Ga Al’ummar Amurka
-
Janairu 18, 2021
Masu Sharhi Sun Kwatanta Matakan Tsaro A Washington Da Na Tarihi
-
Janairu 17, 2021
Wani Ayarin Baki Masu Kaura Na Dosar Amurka Daga Honduras
Facebook Forum