'Yan Hamayya a Nijar Suna Kokarin Tsige PM Kasar

Tambarin Jamhuriyar Nijar

Tuni aka fara muhawara kan yunkurin tsige PM Briji Rafini na jamhuriyar Nijar.

Idan za'a iya tunawa 'yan hamayya su fiyeda 24 suna gabatar da bukatar neman tsige PM kan zargin aikata rashin gaskiya a gwanatin.

An fara muhawara kan wannan batu. Wakilin Sashen Hausa a Niamey Abdoulaye Mammane Ahmadou, a tattaunawarsa da Maryam Dauda, yace, 'yan hamayyar suna zargin an sayawa shugaban kasa jirgin sama ba tareda bin ka'ida ba, da kuma sama da fadi da dukiyar jama'a.

Idan har 'yan hamayyar suka sami rinjaye a wannan yunkuri,ba da jumawa ba wannan gwamnati da PM Briji zata sama tarihi.

A gefe daya kuma, wata kotun kasar ta saki mutane 17 cikin wadanda ake tsare dasu kan zargin safarar jarirai.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Hamayya a Nijar Suna Kokarin Tsige PM Kasar