Accessibility links

Ana ci Gaba da Cece-Ku-Ce Kan Sefa Miliyan Dubu 400 da Tandja Yace ya Baria Baitulmalin Nijar

  • Garba Suleiman

Mamadou Tandja

Manyan hafsoshin Jandarma na Nijar sun bukaci jin bahasi daga bakin tsohon shugaban kan wannan kudin da yace ya bari a baitulmali kafin a yi masa juyin mulki.

Har yanzu ana ci gaba da cece-ku-ce a fagren siyasar Jamhuriyar Nijar a sanadin kalamun da tsohon shugaba Tandja Mamadou yayi cewa akwai kudi har Sefa miliyan dubu 400 a cikin baitulmalin gwamnatin kasar kafin a yi masa juyin mulki.

Magoya bayan tsohon shugaba Tandja sun yi cinciurindo a gidansa jiya asabar da safe, domin jin yadda zata kaya a game da takardar da manyan hafsoshin jandarma na Nijar suka rubuta cewar su na son zuwa jin bahasin wadannan kudaden da shi tsohon shugaban yace ya bari kafin a hambarar da gwamnatinsa ranar 18 ga watan Fabrairun shekarar 2010.

Lauyan tsohon shugaban yace ai gwamnatin yanzu ta ce zata gudanar da bincike, kuma kowa ya san hanyar gudanar da bincike, tunda akwai takardu na abubuwan da suka shiga aljihun gwamnati da wadanda suka fita.

Abdoulaye Mamane Ahmadou ya aiko da cikakken rahoto na wannan dambarwar.

XS
SM
MD
LG