'Yan Majalisun Arewacin Najeriya Sun Goyi Bayan Yiwa Mayaka Ahuwa

Irin hare-haren da ake zargin kungiyar Boko Haram da kaiwa a kusan duk fadin arewacin Najeriya

Shugabannin majalisun arewacin Najeriya goma sha tara sun gudanar da wani taro a Minna fadar gwamnatin jihar Naija da nufin ci gaban da neman hanyar maido da zaman lafiya a yankin.

A cikin hirar da suka yi wa da wakilinmu Mustapha Nasiru Batsari, 'yan majalisar sun bayyana goyon bayan yunkurin gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan na yiwa kungiyar mayakan Jama'atu Ahlussunah Lidda'awati Wal Jihad da aka fi sani da suna Boko Haram ahuwa, suka kuma yi kira da a ba gwamnatin kyakkyawan goyon baya domin ganin haka ta cimma ruwa.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Majalisun Arewacin Najeriya Suna Neman Hanyar Zaman Lafiya A Yankin