Accessibility links

Hukumar Shige Da Ficen Najeriya Ta Cika Shekaru 50

  • Grace Alheri Abdu

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya, a taron kungiyar ECOWAS ko CDEAO.

Shugaban hukumar, Rilwanu bala Musa, ya tattauna da Muryar amurka kan tazarar da hukumar ta cimma a shekaru 50 da kafuwarta

Shugaban hukumar shige da ficen Najeriya Rilwanu Bala Musa ya bayyana cewa, paspo din Najeriya shine yafi kowanne inganci a kasashen duniya sabili da daukar hoton yatsun mutum da ake yi dake bada damar samun bayanai a kanshi duk inda ya shiga a duniya.

Shugaban hukumar shige da ficen ya bayyana cewa, Najeriya ce ta farko a kasashen nahiyar Afrika da ta fara gabatar da takardar paspo ta zamani da ake dauka da na’urar computa da ake kira E-Passport wadda mutum ba zai iya canzawa.

Mal Rilwanu ya kuma bayyana cewa, hukumar ce ta farko da ta fara gabatar da tsarin biyan kudin aikin da gwamnati ke yi ta banki da nufin ganin cewa, kudin gwamnati ya shiga aljihun gwamnati.

A cikin hirarshi da manema labarai yayinda ake cika shekaru 50 da kafa hukumar, --- ya bayyana cewa, hukumar tana da ofisoshi a dukan kananan hukumomin Najeriya duk da kalubalai da hukumar ke fuskanta.
XS
SM
MD
LG