ZABEN 2015: Murnar Nasarar Buhari Ta Kai har Kamaru

Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari

Tunda aka bada labarin cewa Janar Muhammad Buhari ne ya lashe zaben Najeriya murna ta barke a kasar Kamaru

Al'umman Kamaru suna ta cewa barka barka yayinda kowa na ba dan'uwansa hannu.Mutane na cewa an yi nasara an kuma samu nasara.

Wani malami a birnin Yarwa ya bayyana farin cikinshi da nasarar Janar Muhammad Buhari. Nasarar abar godewa Allah ce. Yace maganar rashin tsaro da cin hanci da rashawa sun kare domin lokacin da Buhari ya yi mulki ya yi adalci ya kuma tsare gaskiya. Yanzu ma da zai dawo zai yiwa mutane adalci.

Abun da yakamata Janar Buhari ya soma dashi shi ne tsaro. Idan aka kare lafiyar mutane da dukiyoyinsu abubuwa zasu zo da sauki. Mutane da dama sun bar gidajensu domin an kashe masu 'yan uwa an kuma lalata muhallansu.

Ga rahoton Muhammad Danda

Your browser doesn’t support HTML5

ZABEN 2015: Murnar Nasarar Buhari Ta Kai Har Kamaru - 2' 14"