Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2015: Murnar Nasarar Janar Buhari Ta Hallaka Mutane Biyu a Neja


Janar Buhari mai jiran gadon mulkin Najeriya

Gwamnatin jihar Neja ta kafa dokar ta baci sabili da mutane da suka fantsama kan hanyoyi a biranen jihar suna murnar nasarar Janar Buhari sun soma bata kadarorin gwamnati da ma salwantar rayuka

Masu murnar nasarar Janar Buhari sun soma wuce gona da iri domin mutane sun fara lalata kayan gwamnati har ma da mutuwar wasu.

Rahotanni daga Kwantagora sun tabbatar da mutuwar mutane biyu a lokacin zanga-zangar murnar. Sakataren gwamnati ya bayyana cewa gwamnati ta dauki matakin takaita zirga-zirgan jama'a domin hana yaduwar tashin hankali da barna.

Dubban jama'a suka bazu a manyan titunan biranen jihohin Neja da Kogi suna farin cikin samun nasarar Janar Buhari a zaben da aka gudanar ranar Asabar da ta wuce.

A jihar Neja matasa maza da mata suka dinga wasa da ababen hawa tare da matsa hon. A tsakiyar birnin Minna mutane suna ta yin wasa da babura. Wani Muhammad Sani Tijjani yace suna yin murna ne domin nasarar da Ubangiji ya baiwa Janar Buhari.

A Lokoja fadar gwamnatin jihar Kogi labarin daya ne. Wani Ishaq Imam ya bayyana abubuwan dake faruwa. Mutane da dama sun fito suna murna domin nasarar da Janar Buhari ya samu.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00
Shiga Kai Tsaye

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG